wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
'Yan Koriya sun bukaci a biya su diyya saboda wasan Ronaldo

Masoya kwallon kafa a Koriya ta Kudu na neman a biya su diyya bayan Cristiano Ronaldo ya gaza bayyana akan fili domin buga wani wasan share fagen shiga sabuwar kakar wasanni a makon jiya a birnin Seoul.
Bayanai sun ce, an yi yarjejeniyar cewa, Ronaldo zai buga wasan na tsawon minti 45 kamar yadda masu shirya gasar K-League All Stars ta Koriya ta Kudun suka sanar, amma ya bige da zama a banci.
Masoya kwallon kafar kasar sun fara bayyana fushinsu bayan sun fahimci cewa, gwarzon dan wasan bai ma nuna alamar daura takalminsa ba, abinda ya sa suka fara wake-waken kiran sunan Lionel Messi don nuna wa Ronaldo adawa.
Yanzu haka wasu daga cikin masoya kwallon sun fara shigar da kara, inda suke neman a biya su diyyar Dala 59 akan kowanne tikitin da suka saya domin kallon wasan Ronaldo.