rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Liverpool ta sayo tsohon mai tsaron ragar WestHam United

media
Sabon mai tsaron raga Adrian da Liverpool ta sayo don maye gurbin Mignolet Liverpool.FC

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kammala sayen tsohon mai tsaron ragar West Ham United Adrian da nufin maye gurbin Simon Mignolet, da ya sauya sheka zuwa Club Bruges.


Adrian, mai shekaru 32, wanda ya karkare kwantiraginsa da WestHam a wannan Kaka, zai taka rawar zabi na biyu a matsayin mai tsaron ragar Liverpool bayan Alisson Becker da ke matsayin zabin farko na Liverpool.

Tun bayan da Adrian ya kulla kwantiragi da WestHama a shekarar 2013 daga Real Betis ya tsarewa West Hama raga a wasanni 150 cikin shekaru 6.

Cikin wannan kaka ce dai, Liverpool din ta raba gari da Mignolet wanda yakoma Brudges kan yuro miliyan 6 da rabi.

Bayan rattabu hannu kan yarjejeniyar, Adrian ya ce ya na fatan taimakawa Liverpool dage kofin gasa daban-daban a wanan kaka.