rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Leroy Sane zai yi jinyar watanni shida zuwa bakwai'

media
Leroy Sane da Pep Guardiola a Wembley Reuters

Kocin Manchester City pep Guardiola na sa ran Leroy Sane zai rasa damar taka leda har tsawon watanni shida zuwa bakwai sakamakon raunin da ya samu a guiwar kafarsa.


Sane mai shekaru 23 ya gamu da raunin ne a yayin gasar Community Shield da Manchester City ta samu nasara akan Liverpool a Wembley a ranar Lahadin da ta gabata.

Dan wasan ya fice daga fili bayan shafe minti 13 kacal akan filin wasan na Wembley, yayinda ake sa ran yi masa tiyata a birnin Barcelona a mako mai zuwa.

Raunin Sane dan asalin Jamus na zuwa ne a daidai lokacin da ake fara  sabuwar kakar gasar firimiyar Ingila, inda a gobe Asabar, kungiyarsa ta Manchester City za ta barje gumi da West Ham.

A cewar Guardiola, ba shi da masaniya game da tsawon jinyara da Sane zai yi, amma ya ce, irin wannan raunin na kaiwa watanni shida zuwa bakwai kafin warkewa.