rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Barcelona na gab da sayen Neymar daga PSG

media
Neymar na Brazil REUTERS/Philippe Wojazer

Mahukuntan Barcelona sun kama hanyar zuwa birnin Paris na Faransa a wannan Talata domin tattaunawa da PSG game da kammala sayen Neymar na Brazil.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, har yanzu Real Madrid, babbar abokiyar hamayyar Barcelona, na da burin sayen dan wasan, kuma ana ganin muddin ta yi nasarar sayen shi, to za ta jingine batun dauko Paul Pogba daga Manchester United kamar yadda Jaridar Sun ta rawaito.

Kazalika jaridar Marca ta rawaito cewa, Lionel Messi ya gana da Neyma ta wayar tarho da zummar shawo kansa don ganin ya dawo Barcelona a maimakon tafiya Real Madrid.

A gefe guda,PSG tuni ta dakatar da sayar da riguna masu dauke da lambar Neymar a shagonta, abinda ke dada nuna cewa, kungiyar a shirye take ta sallama shi.