rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Chelsea ta shirya doke Liverpool a gasar Super League

media
Kocin Chelsea Frank Lampard Reuters/Ed Sykes

Yau ne za a kara tsakanin Chelsea da Liverpool a gasar Super League a birnin Santanbul na Turkiya, wasan da kocin Chelsea ya bayyana cewa, sun shirya masa.


Gabanin wannan haduwa, kocin Chelsea, Frank Lampard ya bayyana cewa, ya dauki darasi kan kashin da kungiyarsa ta sha a hannun Manchester United a ranar Lahadin da ta gabata, yayinda ya kalubalancin ‘yan wasansa da su mayar da martani akan Liverpool a karawarsu ta yau.

Manchester United ta zazzaga wa Chelsean kwallaye 4-0 a Old Trafford, kuma ana ganin matsalar tsaron baya ce ta janyo aka yi musu wannan zazzagar a raga.

Shi ma kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya shaida wa ‘yan wasansa da su kara nuna yunwarsu ta lashe kofuna a wannan sabuwar kakar bayan kofun zakarun Turai da suka lashe a kakar bara.

A gafe guda, Kloop ya bayyana cewa, mai tsaren ragarsu Alisson zai yi zaman jiyar makwanni biyo bayan raunin da ya samu a kafarsa a yayin wasansu na farko da suka samu nasara akan Norwich City a gasar firimiya.

Golan dan asalin Brazil mai shekaru 26, ya fice daga fili bayan shafe minti 39, inda sabon golan da Liverpool ta yi cefanansa a wannan kaka wato, Adrian ya maye gurbinsa.