rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ba ma fargabar jadawalin gasar zakarun Turai- Klopp

media
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp Reuters

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce bai sa a ransa dole sai Club din ya sake dage kofin zakarun Turai a bana ba, bayan nasararsa ta dage kofin a bara da nasarar kwallaye 2 da banza kan Tottenham.


A cewar Klopp wanda ke jawabin gabanin fitar da jadawalin gasar a yau, ya ce akwai kungiyoyi da dama da suka cancanci dage kofin ba Liverpool kadai ba.

Jurgen Klopp ya ce baya fargabar kai wa wasan karshe na bana karkashin gasar cin kofin na zakarun Turai da zai gudana ranar 30 ga watan Mayun 2021 filin wasa na birnin Santanbul da ke turkiya, sai dai ya ce Liverpool na da cikakkiyar dama ne kwatankwacin wadda kowanne Club cikin kungiyoyin kwallon kafa 26 da za su fafata a gasar ke da shi.

Kalaman na Klopp dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Liverpool din ke jerin tawagar farko da ake kyautata zaton iya lashe kofin na bana.

Rukunin farko dai da hasashen ya nuna cewa za su iya dage kofin sun kunshi ita Liverpool din kana Barcelona wadda Livertool ta fitar a wasan gab dana karshe a bara, sai kuma Manchester City babbar abokiyar dabin Liverpool kuma mai rike da kofin Firimiya kana PSG Juventus Real Madrid dsa kuma Tottenham wadda tasha kaye hannun Liverpool a wasan karshe na dage kofin.