rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Ingila Italiya Seria A

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sanchez ya isa Italiya don soma takawa Inter Milan leda

media
Alexis Sanchez. Reuters/Carl Recine

Dan wasan gaba na Manchester United Alexis Sanchez ya isa birnin Milan na Italiya, inda ake sa ran zai sa hannu kan yarjejeniyar komawa kungiyar Inter Milan a matsayin aro tsawon shekara daya.


Sanchez zai sake haduwa da abokin wasansa a United wato Romelu Lukaku, wanda ya sauya sheka zuwa kungiyar ta Inter Milan kan euro miliyan 65.

A watan Janairu na 2018, Sanchez ya koma United daga Arsenal, sai dai bayan buga mata wasanni 32, kwallaye 3 kawai dan wasan ya ciwa kungiyar.