Kungiyoyin kwallon kafa a Ingila na so a jinkirta rufe kasuwar 'yan wasa
Kungiyoyin da ke wasa a gasar firimiyar Ingila na iya kada kuri’ar jinkirta rufe kasuwar hada- hadar ‘yan wasa kafin fara gasar a taron su na 12 ga Satumba.
Wallafawa ranar:
Shekaru biyu da suka gabata, kungiyoyin suka kada kuri’ar goyon bayan rufe kasuwar kafin a fara gasar sabuwar kaka don rage matsalar da ake samu a tawagogin kungiyoyin.
Sai dai saura kasashen ba su bi sahun kungiyoyin gasar firimiyar Ingila ba, saboda haka suna da damnar sayen ‘yan wasa ko kuma karbar aron su a gasar firmiyar Ingila.
Kungiyoyin sauran gasannin na kaiwa har 2 ga Satumba kafin su rufe tasu kasuwar hada – hadar, sabanin 8 ga Agusta da gasar firimiyar Ingila ke rufe ta ta kasuwar.
Kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito, za a gudanar da taron shugabannin kungiyoyin gasar firimiya a mako mai zuwa, inda za su dauko batun.
Shugabannin kungiyoyin na firimiyar Ingila na iya kada kuri’a kuma don jinkirta rufe kasuwar don ta ci daidai da sauran takwarorinsu a Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu