rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Messi na shirin raba gari da Barcelona

media
Lionel Messi Reuters/Lee Smith

Wata Jaridar wasanni ta Mundo Deportivo a Spain ta ruwaito cewa dan wasan Argentina kuma Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi na duba yiwuwar komawa Amurka da taka leda bayan ko kuma gabanin karkarewar kwantiraginsa da Barcelona.


Messi mai shekaru 32 wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or har sau 5, karkashin kwantiraginsa na da zabin iya raba gari da Barcelona a kowacce karshen kaka gabanin karkarewar wa’adinsa.

Akwai dai bayanan da ke cewa Messi na shirye-shiryen bin David Beckham zuwa Inter Miami can a Amurka, inda kuma suka yi alkawarin bashi kwantiragin marar iyaka wato har karshen rayuwarsa.

Sai dai tuni Barcelona wadda a shekarar 2021 kwantiraginta da Messi zai zo karshe ta mikawa dan wasan bukatar tsawaita kwantiragi har karshen rayuwarsa don nesanta masa tunani da barin club din.