rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ronaldo ya sake kafa tarihi a Turai bayan zura kwallo 4 a wasa daya

media
Cristiano Ronaldo dan wasan Juventus da Portugal 路透社

Cristiano Ronaldo na Juventus ya sake kafa tarihi bayan zura kwallaye 4 a raga yayin wasan da Portugal ta lallasa Lithuania da kwallaye 5 da 1.


Nasarar ta Ronaldo ta bashi damar goge tarihin da takwaransa na Ireland Robbie Keane ya kafa bayan da yanzu haka ya ke da yawan kwallaye 25 a wasannin neman gurbin makamanciyar gasar ta cin kofin Turai.

Gabanin fara wasan dai a jiya, Ronaldo ya sanya hotunan kyautukansa na Ballon d’Or 5 a Instagram inda Keane wanda abokin Ronaldon ne ya ke masa wasa da cewa ya kafa tarihi da yawa kamata yayi ya barwa na baya.

Wannan dai ne karo na 8 da Ronaldo ke zura kwallo 3 ko fiye da haka a bangaren kasarsa Portugal, haka zalika bayan zura kwallayen na jiya yanzu haka Ronaldo na da adadin kwallaye 93 da ya zurawa kasarsa bugu da kari shi ne dan wasa daga Nahiyar Turai daya tilo da ya taba zura kwallaye fiye da 90 ga kasarsa.