rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kwando

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta fitar da Amurka a gasar kwallon kwando duniya

media
Tawagar kwallon kwando ta Faransa Nicolas ASFOURI / AFP

Mai rike da kambun gasar cin kofin kwallon kwando ta Duniya Amurka, ta sha mamaki bayan Faransa ta doke ta 89-79 a matakin wasan daf – da – na- kusa – da - karshe a jiya Laraba a gasar da ke gudana a China yanzu haka.


Tawagar kwallon kwandon Amurkan ta lashe kofin gasanni biyu na gasar da suka gabata, kuma ba a doke ta a wasanni 58 na kasa – da – kasa ba tun a shekarar 2006.

A zubi na uku na wasan, Faransa ke kan gaba da kwallaye 51-41, amma Amurka ta yunkuro wasa ya zama 72-65,daga bisani Faransa ta dage har ta yi nasara a wasan.

Faransa zata kara da Argentina a wasan kusa da na karshe gobe Juma’a.