rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Valencia ta sallami Marcelino

media
'Yan wasan Valencia da Real Madrid a karawarsu a filin wasa na Stade Mastella 2014 AFP/Jose Jordan

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia a Spain, ta sallami kocinta Marcelino kuma ta maye gurbinsa da tsohon dan wasan Real Madrid, wadda shi ne mataimakinsa Albert Celades.


Dan shekara 54 din ya koma kungiyar ne a 2017, kuma bayan kakar wasan kungiyar ta jera shekaru biyu tana karkare gasar La ligar Spaniya a matsayi na 12.

Yanzu tsohon dan wasa tsakiya na Real Madrid mai shekaru 43, ya karbi ragamar horar da kungiyar daga yanzu zuwa shekarar 2021 kuma a jiya Laraba ya yi atisayensa na farko.

A shekaru biyu daya yi a kungiyar, Marcelino ya kai kungiyar kammalawa a ta hudu a gasar La liga, lamarin da ya ba ta damar fafatawa a gasar zakarun nahiyar Turai.

Tsohon kocin na Sevilla da Villarreal ya ci wa kungiyar kofin Copa Del Rey a kakar da ta gabata, babban kofin ta na farko a cikin shekaru 11.