rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ter Stegen ya cire wa Barcelona kitse a wuta

media
Mai tsaron ragar Barcelona Andre Ter Stegen Reuters

Mai tsaron ragar Barcelona Marc-Andre ter Stegen ya ceto bugun daga – kai – sai – mai- tsaron raga da Marco Reus' ya buga a wasan da Barcelona ta rike Borussia Dortmund canjaras babu ci, a wasan farko na gasar zakarun nahiyar Turai duka a daren jiya Talata.


Mai taron ragar dan asalin Jamus ya sake hana Reus jefa kwallo a ragarsa har sau biyu yayin da Dortmund ta mamaye wasan a zubi na biyu bayan hutun rabin lokaci.

Saura kiris Julian Brandt ya saka kwallo a raga kusan karshen wasa, saboda ta wuce Ter Stegen amma sai ta daki turke.

Barcelona ta baiwa dan shekara 16 nan, Ansu Fati damar wasa, sai dai babu abin a zo – a –gani da hakan ya haifar, kuma duk da cewa Lionel Messi ya shiga wasan daga baya.

SAURA SAKAMAKON WASANNIN DAREN TALATA

Napoli 2     0 Liverpool

Salzburg 6   2 Genk

Inter 1     1 Slavia Prague

Lyon 1     1 Zenith St Petersburg

Benfica 1     2 RB Leipzig

Ajax 3    1 Lille

Chelsea 0    1 Valencia