rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Arsenal ta fara Europa da kafar dama

media
Wasu daga cikin 'yan wasan Arsenal Reuters/Andrew Boyers

Kwalaye daga ‘yan wasan da ba a dade da yayewa daga tawagar matasa ta Arsenal ba, wato Joe Willock da Bukayo Saka sun taimaka wa Arsenal din a wasa mai sarkakiya da ta fafata da Eintracht Frankfurt a gasar zakarun Turai ta Europa a daren Alhamis, lamarin da ya sa ta fara gasar ta wannan kaka da kafar dama.


Willock ya ci wa Arsenal kwallon ta ta farko a wasan sakamakon kwallon da ta daki jikin dan wasan Frankfurt, kafin Saka ya saka kwallo ta biyu a minti na 85 na wasan.

Minti biyu bayan wannan kwallo, Pierre-Emerick Aubameyang ya kara ta uku, lamarin da ya kawo karshen rashin nasara da dasaura kiris ta jera wasanni uku tana yi.

Arsenal ta samu karin damammaki amma ita ma din sai da mai tsaron ragarta Emiliano Martinez ya rufa mata asiri saboda ‘yan wasan bayanta sun yi bacci.

Mai tsaron ragar dan kasar Argentina ya hana kwallayen Filip Kostic and Andre Silva shiga raga a zubin farko na wasan.