rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ko wani hali Messi ke ciki bayan ya samu sabon rauni?

media
Lionel Messi a sunkuye a filin wasa na Camp Nou Reuters

Gwarzon dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya samu rauni a cinyarsa a fafatawar da kungiyarsa ta doke Villarreal da kwallaye 2-1 a a gasar La Liga a Camp Nou.


Messi wanda a kwanan nan ya murmure daga wani rauni da ya samu a kafarsa, an sauya shi da Ousmane Dembele bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan na jiya.

Kodayake kocin Barcelona ya bayyana raunin na Messi a matsayin wata karamar matsala, yana mai cewa, idan wani abu ya samu dan wasan, to hakan zai shafi kowa a kungiyar.

Dan wasan shi ne ya bugo kwallon da Antoine Griezmann ya jefa da ka a ragar Villarreal a cikin mintina shida da soma wasan , yayin da Arthur ya kara ta biyu a minti na 15.

A bangare guda, kungiyar Granada wadda ta kasance bakuwa a gasar ta La Liga ta bana, ta dare saman teburin gasar bayan ta yi kunnen doki 1-1 da Real Valladolid.

Yau ne Real Madrid za ta kece raini da Osasuna, yayin da Athletic Bilbao za ta kai ruwa rana da Leganes.