rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Alisson Becker na Liverpool ya murmure daga jinya

media
Mai tsaron ragar Liverpool, Alisson Becker Liverpool.FC

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce mai tsaron ragar Club din Alisson Becker na gab da murmurewa daga raunin da ya samu, inda ake sa ran ya taka leda a wasansu da Lesta City ranar Asabar gabanin wasansu da Manchester United.


Alisson mai shekaru 26 wanda yanzu haka shi ne mai tsaron raga mafi kwarewa yanzu a duniyar kwallo, ya rasa wasannin Liverpool har guda tara tun bayan samun rauni a wasansu na farko da suka kara da Norwich ranar 9 ga watan Agusta.

A gobe Laraba ne, Liverpool za ta kara da Red Bull Salzburg a gasar zakarun Turai, gasar da za a iya cewa ta zowa Club din a bai-bai duk da kasancewarsa mai rike da kambunta.

A cewar Klopp Liverpool yanzu haka gwarzon mai tsaron ragar ya fara halartar filin atisaye a yau Talata, kuma suna sa ran bangaren masu kula da lafiya na Club din su bashi izinin fara taka leda.

Bayan wasan Liverpool da Lesta da kuma gajeran hutun da kungiyoyin kwallon kafar za su fara, a ranar 20 ga watan Octoba ne za ta kara da Manchester United karkashin gasar zakarun Turai.