rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tauraruwar Ronaldo da Messi na gab da daina haskawa

media
Cristiano Ronald na Portugal da Lionel Messi na Argentina Josep LAGO / AFP

Makwanni 7 da fara sabuwar kakar wasa har yanzu zakarun ‘yan wasan nan biyu wato Cristiano Ronaldo na Portugal mai taka leda a Juventus da Lionel Messi na Argentina mai taka leda a Barcelona kwallaye 3 kacal kowannensu ya iya zurawa Club dinsa.


‘Yan wasan biyu wadanda suka mamaye duniyar kwallo shekaru 10 da suka gabata sun yi nasarar zura kwallaye dubu 1 da 369 baya ga lashe kyautar Ballons d’Or har guda 10 a tsakaninsu, to amma wani sharhin jaridar wasanni ya nuna cewa da alamu haskensu na gab da dishewa a fagen tamaula.

Wannan dai ne karon farko tun bayan kakar wasa ta 2005 da ‘yan wasan biyu wato Ronaldo da Messi suka zura kwallaye kasa da biyar daga farkon kaka a watan Agusta zuwa karshen Satumba.

Tun a farkon wannan kaka, Messi mai shekaru 32 ke fuskantar raunuka daban-daban wanda ya hana masa taka leda a wasannin Club dinsa,inda a bangare guda Ronaldo mai shekaru 34 ya gaza nasarar zura kwallaye kamar yadda ya saba.