rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Alkalin wasa bai kyauta mana ba - Conte

media
Antoine Griezmann na Barcelona da Diego Godin na Inter Milan yayin karawarsu a daren Laraba. Montage REUTERS/AFP

Kocin Inter Antonio Conte ya caccaki alkalin wasa, bayan doke tawagarsa 2-1 da Barcelona ta yi a jiya Laraba.


Bayan dan wasan Inter Laurataro Martinez ya sanya kungiyarsa a gaba da kwallo daya da ya ci a cikin minti na biyu da fara wasa, Suarez ya ci kwallaye biyu bayan hutu, wasa ya tashi 2-1.

Amma Conte ya na ganin ba a mai adalci ba, don an wa tawagarsa coge.

Conte wanda ya sha kashedi daga alkalin wasa saboda yadda ya yi ta yin mazurai ga alkalin wasan, yana ganin kamata yayi a ba tawagarsa bugun daga – kai - sai – mai - tsaron raga lokacin da aka rafke dan wasan sa Stefano Sensi amma alkalin wasa ya dauke kai.