rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Liverpool ta sha da kyar

media
Mai horar da 'yan wasan Liverpool Jurgen Klopp Phil Noble/Reuters

Liverpool ta sha da kyar a hannun Red Bull Salsburg a daren Laraba a kokarin da ta ke na kare kambunta a gasar zakarun nahiyar Turai a gidanta Anfield.


Tun da farko sai da Liverppol din ta antaya wa bakin nata kwallaye uku a raga amma suka dage, har suka farke dukkannin kwallayen, wasa ya zama 3-3 kafin daga bisani Mohamed Salah ya jefa kwallo daya a ragar Salsburg bayan an dawo hutu.

Liverpool dai ta yi rashin nasara a wasan ta na farko a gasar ta bana a rukuni na 5 sakamkon doketa da Napoli ta yi, amma ta yunkuro a wannan wasa bayan tsohon dan wasan Salsburg da ke mata wasa a halin yanzu, wato Sadio Mane, ya fara saka kwallo a cikin minti 10 da fara wasan na jiya Laraba, Andrew Robertson ya ci kwallo ta 2, yayin da Mohamed Salah ya ci ta 3 da ta 4 wasa ya tashi 4-1.

Salsburg ta nuna wa Liverpool cewa ba kawan lasa take ba, saboda a wannan kaka kawai ta ci kwallaye 40 a wasanni 9, saboda haka ta farke wadannan kwallaye cikin ruwan sanyi.