rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mun ji kunyar lallasa mu da Bayern Munich ta yi - Vertonghen

media
'Yan wasan Tottenham suna murnar cin kwallo Reuters

A daren Talata, a gasar zakarun nahiyar Turai, Tottenham ta bari Bayern Munich ta yi mata dukan kawo wuka da kwallaye 7 da 2.


Wannan lamari ya sa dan wasan baya na Tottenham din, Jan Vertonghen ya ce babu abin kunyan da ya kai haka, saboda har gida aka bi su aka antaya musu wadannan kwallaye, kuma dole haka ya hana su bacci.

Da farko dai kamar Tottenham za ta yi rawar gaban hantsi, inda har ta fara jefa kwallo a ragar Bayern, amma sai Bayern Munich din ta nuna kwarewa da rashin tausayi, ta rika antaya kwallaye a ragar Tottenham har sai da suka kai bakwai !