rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nasarar Liverpool barazana ce ga Manchester City- Gundogan

media
Ilkay Gundogan dan wasan Manchester City Yahoo Sport UK

Dan wasan tsakiya na Manchester City Ilkay Gundogan ya ce Club din ya rasa damarmakin da suka bai wa Liverpool sukunin basu tazara mai yawa a teburin Firimiya, sai dai a cewar dan wasan akwai fatan itama Liverpool ta yi rashin nasara a wasu wasanni nan gaba wanda zai bai Cityn damar rage tazarar da ke tsakaninsu.


Gondogan a wata zantawarsa da jaridar wasanni, ya ce yanzu ne kakar wasan ta fara inda ake da sauran wasanni 30 karkashin gasar ta Firimiya, kuma ba lallai Liverpool ta ci gaba a yadda ta faro ba.

City wadda ke rike da kofin Firimiya, rashin nasararta a wasan da suka tashi 3 da 2 da Norwich da shankayenta har gida a hannun Wolves baya ga canjaras da Tottenham su ne suka haddasa mata fuskantar koma baya da ta kai ga Liverpool ta ba ta tazarar maki 8.

Dan wasan na City mai shekaru 28 ya ce ba abu ne mai sauki ga ‘yan wasan Manchester City ba, su ci gaba da kallon babbar abokiyar dabinsu na nasara a wasanninta yayinda su kume ke samun koma baya.

Kalaman Gondogan na zuwa ne bayan na manajan Club din a jiya Litinin Pep Guardiola da ke cewa babu abin daga hankali a tazarar makin da ke tsakaninsu da Liverpool don kuwa akwai kyawawan ranaku a tafe.