Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

An dakatar da wasannin kwallon kafa a Catalan

Hukumar kwallon kafa ta yankin Catalan ta dakatar da duk wata harkar kwallon kafa a yankin a yau Litinin bayan hukuncin dauri da aka yanke wa wasu shugabannin ‘yan awaren yankin.

Rikicin siyasar Catalonia
Rikicin siyasar Catalonia rfi
Talla

Kotun kolin Spain ta yanke wa jagororin hukuncin ne sakamakon rawar da suka taka a batun zaben raba gardama na shekarar 2017.

Hukumar kwallon kafar yankin ta ce ta yi dakatarwar ce don nuna goyon baya ga jagororin ‘yan awaren da iyalensu, kuma ta shafi dukkannin wasanninta a hukumance, sai dai ban da wasannin Laliga na Spain.

Catalonia dai yanki ne mai ‘yar kwarya – kwaryar gashin kai a arewa maso gabashin Spain wacce a ranar 1 ga watan Oktoban 2017 ta gudanar da zaben raba gardama inda kashi 90 na masu zaben suka zabi a ba Catalonia yancin kai.

Hukuncin na ranar Litinin na zuwa ne bayan an yi watanni hudu ana shari’a.

A watan Maris na shekarar 2018, an ci tarar kocin Manchester City sakamakon sanya wani kambu mai ruwar daurawa, wata alama ta nuna goyon baya ga samun yancin yankin Catalonia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.