Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Manchester United za ta sayi Mandzukic

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na daf da sayen dan wasan gaba na Juventus Mario Mandzukic da zarar an bude kasuwar hada – hadar ‘yan wasa ta watan Janairu.

Mario Mandzukic dan wasan Juventus da Croatia
Mario Mandzukic dan wasan Juventus da Croatia REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Kungiyar ta Ingila na da kwarin gwiwar cewa Juventus zata karbi fam miliyan 9 saboda ta kosa ta sayar da dan kasar Croatia din.

Ana sa ran Mandzukic ya sanya hannu a kwantiragin watanni 18 har zuwa shekarar 2021, kuma za a rika biyansa albashin fam miliyan kusan 4 da rabi duk shekara.

Manchester United ta kasa cin fiye da kwallo daya a wasa tun bayan doke Chelsea 4-0 a makon farko na gasar Firimiyar Ingila.

Yanzu matsayi na 12 suke a teburin gasar Firimiya a wannan kaka da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.