Isa ga babban shafi

Wariyar launin fata: Sau biyu ana tsayar da wasan Ingila da Bulgaria

Sau biyu ana tsayar da wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Turai tsakanin Ingila da Bulgaria a daren jiya Litinin domin yi wa magoya bayan Bulgaria kashedi sakamakon kalaman nuna wariyar launin fata da suka yi ta yi tare da yin kukan birrai, gami da salon sarawa na sojin Nazi.

Kocin Ingila, Gareth Southgate.
Kocin Ingila, Gareth Southgate. DR
Talla

An tsayar da wasan ne karon farko a minti na 28, yayin da Ingila ke kan gaba da ci 2-0, inda aka yi Allah wadai da wannan dabi’a ta magoya bayan Bulgarian ta wajen wata yekuwa da masu tafiyar da wasan suka yi ta amsa kuwwa, kana aka ci gaba da wasa.

A minti na 43 da wasa aka sake tsayar da wasan, aka kuma ci gaba bayan ‘yar tattaunawa tsakanin alkalin wasa da mai horar da tawagar kwallon kafar ingila, Gareth Southgate.

Sai dai duk da wannan cin fuska ta wajen nuna wariya, ‘yan wasan Ingila ba su yi kasa a gwiwa ba, inda suka rika antaya wa Bulgaria kwallaye a raga har sai da wasa ya tashi 6-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.