Isa ga babban shafi
Wasanni

Naushi ya hallaka wani dan dambe a Amurka

Wani dan damben Boxin a Amurka Patrick Day ya sheka barzahu bayan kakkarfan naushin da ya sha daga abokin karawarsa a filin wasa yayin gasar zakaran damben kasa zagaye na 10 da ke gudana can a Amurkan.

Patrick Day fitaccen dan Dambe a Amurka
Patrick Day fitaccen dan Dambe a Amurka Reuters/Jon Durr
Talla

Wata majiyar wasanni ta bayyana cewa Day mai shekaru 27 wanda ya lashe kyautar zakaran kasa matakin yara har sau biyu, ya shiga doguwar suma ne tun bayan naushin da ya sha daga Charles Conwell a ranar Asabar din da ta gabata, yayinda kuma a yau ya koma ga mahaliccinsa.

Hukumar da ke kula da wasannin Dambe a jihar Chicago ta tabbatar da mutuwar Patrick Day a yau bayan shafe kwanaki 4 a cikin doguwar suma, yayinda likitoci suka tabbatar da cewa naushin ya taba wani sashe na kwalkwalwarsa ne.

Patrick Day matashin dan Dambe wanda tauraruwarsa ta fara haskawa a shekarar 2013 bayan lashe kyautar gwarzon kasashen yankin Amurka a 2017 cikin watan Yulin da ya gabata ne ya shiga sahun zakakuran ‘yan Dambe 10 na duniya.

Mutuwar Dan Dambe a filin wasa ba inda ko cikin watan Yuli Hugo Santillan dan Argentina mai shekaru 23 sai da ya kwanta dama a filin wasa bayan mugun duka aka, yayinda kwanaki kalilan bayan wannan Maxim Dadashev dan Rasha mai shekaru 28 shima yam utu a filin wasa bayan dukan da ya taba kwalkwalwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.