Isa ga babban shafi

Manchester United ta hana Liverpool kafa tarihi

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta gaza gagarumar nasara kan Manchester United a karawarsu ta jiya karkashin gasar Firimiya, inda aka tashi wasa kwallo daya da daya.

Wasan Liverpool da Manchester United a Old Trafford.
Wasan Liverpool da Manchester United a Old Trafford. REUTERS/Russell Cheyne
Talla

Rashin nasarar ta Liverpool a hannun Manchester United, ya hana Club din kafa tarihin doka wasanni 18 ba tare da anyi nasara akansa ba, kamar yadda Manchester City ta kafa.

Haka zalika rashin nasarar ya rage tazarar da ke tsakanin Liverpool da Manchester City zuwa maki 6 daga 8 da ya ke a baya, duk da cewa dai Liverpool din na ci gaba da rike kambunta a matsayin jagora da maki 25.

Manajan kungiyar kwallon kafar ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce Manchester United na shiryawa duk wani wasa da zai gudana a tsakaninsu don ganin ba ta sha kaye a hannun Liverpool ba.

A cewar Klop ba komi United suka yi a wasan na jiya ba, face tsaro tare da hana 'yan wasan Liverpool masu kai farmaki sakat.

Shekaru 5 kenan dai rabon da Liverpool ta yi nasara akan Manchester United karkashin gasar ta Firimiya, kungiyar da yanzu haka ta ke matsayin ta 13 da maki 10 a teburin gasar.

Shima dai tsohon majanan Manchester United Jose Mourinho ya ce Jurgen Klopp bai yi tsamanin shank aye a hannun Manchester United ba.

Ana dai ganin nasarar ta Manchester United ta tsereatar da aikin mai horar da Club din wanda ake rade-radin korarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.