rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Zakarun Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Neymar da Modric sun gaza shiga takarar kyautar Ballon d'Or

media
Dan wasan Real Madrid Luka Modric tare da Neymar na kungiyar PSG. AP

Tauraron kungiyar PSG Neymar, ya gaza shiga cikin ‘yan wasa 30 da aka zabo domin tantance wanda zai lashe kyautar Ballon d’Or ta gwarzon dan wasan duniya a bana.


Sai dai Cristiano Ronaldo, Lionel Messi da Virgil van Dijik sun sake haduwa a takarar ta neman lashe gagarumar kyautar, kamar yadda ta faru akan kyautar gwarzon kwallon kafa na duniya ta FIFA.

Wasu daga cikin sauran ‘yan wasan da za a tantance sun hada da Sergio Aguero, Sadio Mane da Raheem Sterling, sai kuma Frenkie de Jong.

A watan Disamban shekarar bara, dan wasan Real Madrid Luka Modric ya kawo karshen shekaru 10 da Messi da Ronaldo suka shafe suna raba kyautukan na FIFA da Ballon d’Or a tsakaninsu.

Sai dai shima Modric din a bana, baya cikin ‘yan wasan 30 da mujallar wasannin ta Faransa ta ware cikin wadanda za a zabi wanda zai lashe kyautar ta Ballon d’Or.