rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Real Madrid ta soma tuntubar Mourinho

media
Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane. REUTERS/Juan Medina

Rahotanni daga Spain sun ce Real Madrid ta soma tuntubar tsohon kocinta Jose Mourinho domin sake kulla yarjejeniya da shi, don maye gurbin Zinaden Zidane.


Labarin da jaridar El Chiringuito ta rawaito, ya zo ne kwana guda bayan da Zidane ya ce yawaita sukar salon horaswarsa da ake yi gami da yada jita jitar Mourinho zai maye gurbinsa yana ci masa tuwo a kwarya.

Tun bayan sallamarsa da Manchester United ta yi a watan Disambar bara, zuwa yanzu Mourinho yayi watsi da tayin kulla yarjejeniya da kungiyoyin da suka hada da Benfica da kuma Lyon.

A karshen makon da ya kare, Real Madrid ta sha kaye a hannun Real Mallorca da kwallon 1 mai ban haushi, abinda ya haifar da shakku kan dorewar aikin Zidane, wanda tun bayan sake karbar jagorancin kungiyar ta Madrid, al’amuranta suka gaza komawa kamar lokacin da ya jagorance ta wajen lashe kofunan gasar zakarun Turai uku a jere.