rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasan Clasico ya koma ranar 18 ga watan Disamba

media
Wasan Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid REUTERS/Juan Medina

Hukumar kwallon kafar Spain ta sanya ranar 18 ga watan Disamba a matsayin ranar da wasan Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona zai gudana bayan matakin sauya masa lokaci daga Asabar din nan mai zuwa sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Catalonia.


Wasan wanda tun da farko aka tsara zai gudana a filin wasa na Camp Nou na Barcelona Laliga ta nemi mayar da shi filin wasa na Real Madrid don gudanar da shi a ranar da aka tsara amma kuma Barcelona ta ki amincewa da matakin.

Yanzu haka dai hukumar Laliga ta bayyana cewa za ta shigar da kara kan matakin na hukumar kwallon kafar Spain don kuwa ita ta mika bukatar mayar da wasan ne ko dai ranar 4 ko kuma 7 ga watan Disamba maimakon 18 da hukumar ta zartas.