Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Serie A: Ribery zai sha horo mai tsanani

Dan wasan gefe na Fiorentina, Franck Ribery na iya fuskantar horon dakatarwa na wasannin Serie A da dama bayan hoton bidiyon da aka nuno ya tabbatar da cewa ya ture mataimakin alkalin wasa,a wasan da Lazio ta lalasa Fiorentina da ci 2-1.

Franck Ribery
Franck Ribery REUTERS/Albert Gea
Talla

Tsohon dan wasan na Bayern Munich da ke Jamus ya taimaka Fiorentina ta farke kwallo a minti na 27, amma ya zama dan kallo lokacin da Lazio ta ci kwallo ta biyu data ba ta nasara.

Gabanin kwallon da Ciro Immobile ya saka da ka, a minti na 89th’yan wasan Fiorentina na ganin kamata ya yi alkalin wasa ya yanke hukunci kan wani laifi da aka yi musu, kuma korafin da aka ga Ribery ya ke yi kenan ko bayan da aka tashi wasan.

Hoton bidiyo ya nuno Ribery yana musayan kalamai da mataimakin alkalin wasa, kuma yana tura shi da hannu kafin wani ma’aikacin Fiorentina ya ja shi zuwa wani wuri.

Daga baya jami’en Serie A sun tabbatar da cewa an ba dan wasan jan kati na bayan wasa, kuma akwai yiwuwar za a dade ba a dama da shi ba a gasar.

Tun da farko ana ganin horon dakatarwar da za a yiwa dan kasar Faransan ba zai wuce na wasanni 3 ba, amma hukumar Serie na kokari ne na ganin an daina cin zarafin alkalan wasa, saboda haka yana iya samun horon dakatarwa na wasanni da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.