rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Premier League La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Solkjaer ya janye aniyar kulla yarjejeniya da Bale

media
Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer. Reuters/Andrew Boyers

Majiyoyin a Manchester United sun ce mai horas da kungiyar Ole Gunnar Solksjaer, ya janye aniyar kulla yarjejeniya da dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale, saboda yawaitar jinyar raunukan da dan wasan ke yi.


Tun bayan komawarsa Real Madrid daga Tottenham a 2013, Bale yayi jinyar runukan da ya samu sau 21, abinda yasa wasu ke kiransa da sunan “The Glass” wato Karau, kwalba ko ma Gilashin a hausance.

A kakar bana kuwa wasanni 7 kawai Bale ya bugawa Real Madrid.

A baya bayan nan kungiyar ta yiwa Manchester United tayin mika mata Gareth Bale din mai shekaru 30 da Karin kudi a matsayin musayar kulla yarjejeniya da Paul Pogba.