rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tottenham ta kalubalanci jan katin da aka bai wa Son

media
Lokacin da Son Heung-min na Tottenham ya yi wa Andre Gomes keta a Goodison Park Reuters

Tottenham ta daukaka kara don kalubalantar jan katin da aka bai wa Son Heung-min saboda ketar da ya yi wa Andre Gomes na Everton.


A ranar Litinin ne aka yi wa Gomes tiyata saboda gocewa da tsagewar kashi a lokaci guda da ya samu a wuyan kafarsa ta dama a yayin wasan da kungiyoyin biyu suka tashi 1-1 a gasar fimiyar Ingila.

Son dai ya shiga cikin dimuwa bayan ya ga irin girman raunin da ya yi wa Gomes a Goodison Park a ranar Lahadi.

Da farko, alkalin wasa ya bai wa Son katin gargadi kafin daga bisani ya sauya zuwa jan kati .

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce, ba da gangan Son ya yi wa Gomes ketar ba, yana mai cewa, ya kamata a yi amfani da na’urar taimakawa alkalin wasa wato VAR domin yanke masa hukunci.

Muddin  Tottenham ta gaza samun nasara a daukaka karar da ta yi, Son ba zai buga wasanni da kungiyarsa za ta yi da Sheffield United da West Ham da Bournemouth ba.