Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

'Sabon Neymar' ya kafa tarihi a Real Madrid

Dan wasan gaba na Real Madrid, dan kasar Brazil, Rodrygo ya nuna bajintarsa a gasar lig din kwallon kafa mafi girma a nahiyar Turai da kwallaye uku rigis da ya ci mata a wasan da ta ragargaza Galatasaray da ci 6-0 a daren Laraba.

Dan wasan Real Madrid, Rodrygo gabanin wasan Real da Leganes a 30 ga Oktoba.
Dan wasan Real Madrid, Rodrygo gabanin wasan Real da Leganes a 30 ga Oktoba. © REUTERS/Susana Vera
Talla

Dan shakara 18 ya kasance dan wasa na biyu mafi karancin shekaru da ya jefa irin wadannan kwallaye a gasar zakarun nahiyar Turai bayan tsohon dan wasan Real Madrid Raul Gonzales.

Tuni ma aka mai inkiya da ‘’sabon Neymar’’, ganin yadda kamar Neymar, daga kungiyar kwallon kafa ta Santos da ke Brazil ya taho Spain.

A nahiyar Kudancin Amurka ne kawai aka san wannan dan wasa wadda tsawon sa daidai da Neymar, ba kari ba ragi, kafin tahowarsa Real Madrid a farkon wannan kaka.

Sau biyar Rodrygo ya ci kwallo a wasanni shida na farko da ya buga wa sabuwar kungiyar na sa a dukkan gasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.