Isa ga babban shafi
Wasanni-Najeriya

Anthony Joshua na son dambacewa a Najeriya

Wata jaridar wasanni ta ruwaito zakaran damben Boxing da ya sake lashe kambun duniya a karo na 2 Anthony Joshua na bayyana yiwuwar doka wasanshi nag aba a kasarshi Najeriya don kare kambunsa.

Anthony Joshua zakaran damben Boxing na duniya.
Anthony Joshua zakaran damben Boxing na duniya. Andrew Couldridge/Reuters
Talla

Joshua dan asalin Najeriya wanda bayan nasarasa ta shekaran jiya kan Andy Ruiz na Mexico hatta shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya aike masa da sakon taya murna, Mai Magana da yawunsa ya ce kawo yanzu bai tsayar da inda ya ke fatan doka wasan nag aba ba.

Sai dai wata majiyar wasanni ta ce Joshua zai koma London a yanzu haka don fara shirye-shiryen wasan kare kambunsa inda zai kara da Kubrat Pulev.

Joshua mai shekaru 30 ya ce yana fatan ya doka wasan na matakin duniya a kasarsa Najeriya wasan da zai zamo irinsa na farko da Najeriya za ta karbi bakonci koma wata kasa a nahiyar Afrika tun bayan wasan 1975 da ya gudana a kudancin Afrikan mai taken Rumble in the Jungle da ya wakana tsakanin Mohammed Ali da George Foreman a Kinshasa.

A zantawa da manema labarai Joshua ya ce yana samun kiranye-kiranye daga Jama’a wajen ganin ya kara wasa a Najeriya, amma abu ne da ba lallai ya yiwu ba la’akari da cewa ba a samun wutar lantarki tsawon sa’o’I 24 a kasar, amma dai ko ba komi suna kaunarsa kuma shima yana kaunarsu, hasalima yana fatan amsa gayyatarsu a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.