Isa ga babban shafi
Wasanni

Harry Maguire ya zama sabon Kaftin din Manchester United

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da sunan Harry Maguire a matsayin sabon Kaftin din tawagar, watanni 5 bayan zuwansa Old Trafford daga Leicester City, dai dai lokacin da Kaftin din tawagar Ashley Young ke gab da kammala kulla kwantiraginsa da Inter Milan ta Italy.

Harry Maguire sabon Kaftin din Manchester United.
Harry Maguire sabon Kaftin din Manchester United. © Reuters
Talla

Mai horar da kungiyar ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer da ke tabbatar da Maguire a matsayin sabon Kaftin, ya ce dan wasan mai shekaru 26 ya cancanci jagoranci fiye da sauran takwarorinsa.

‘Yan wasan Club din irinsu Marcus Rashford da David De Gea baya ga Jess Lingard dukkanninsu sun rike mukamin Kaftin din a rashin Ashley Young wanda wasanni 18 kadai ya dokawa Club din a wannan kaka.

Sai dai Solskjaer ya ce Maguire ke da cancantar maye gurbin Ashley da ke kokarin raba gari da Manchester United.

Harry Maguire dan Ingila wanda cikin watan Agustan da ya gabata United ta sayo shi daga Lesta kan yuro miliyan 80 kawo yanzu ya dokawa Red Devils wasanni 29.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.