Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Abu ne mai wuya Liverpool ta baiwa Salah damar zuwa Olympics- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce suna bukatar gamsassun bayanai da shawarwari gabanin bai wa dan wasan gaba na Club din Muhammad Salah damar wakiltar kasarsa a gasar kwallon kafa ta Olympics a Japan.

Dan wasan kasar Masar Mohamed Salah da ke taka leda a Liverpool.
Dan wasan kasar Masar Mohamed Salah da ke taka leda a Liverpool. Reuters/Andrew Couldridge/File Photo
Talla

Gasar ta Olympic da za ta gudana a birnin Tokyo na Japan, an tsara ta ne don ‘yan shekaru 23 amma kasashe na da zabin sanya ‘yan wasan da shekarunsu ya zarce hakan don wakiltarsu wadanda yawansu bai haura 3 a cikin tawaga guda ba.

Haka zalika karkashin dokokin FIFA game da gasar hukumar ta bayyana cewa kungiyoyi na da zabin iya bari ko kuma hana ‘yan wasnsu wakiltar kasashensu matukar ya ci karo da wasanninsu na Lig.

Salah mai shekaru 27 wanda na cikin ‘yan wasa 50 da a cikinsu ake saran zabar wadanda za su wakilci kasar a gasar, sai dai ranar karshe ta wasannin gasar ya ci karo da ranar da za a bude wasannin gasar Firimiya na kakar 2020-2021.

A cewar Klopp yayin zantawarsa da manema labarai, abu ne mai wuya Liverpool ta iya baiwa Salah damar barin Ingila ana tsaka da wasannin kaka, amma dai yana son tattaunawa sa Salah kan batun, wanda ya ce kawo yanzu babu wanda ya tuntubeshi daga bangaren dan wasan ko kasarshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.