Isa ga babban shafi
Wasanni

Amokachi ya zama babban jami'in NFF

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya ta nada tsohon tauraron kwallon kafar kasar Daniel Amokachi a matsayin shugaban kula da sashen tsare-tsare na hukumar.

Daniel Amokachi
Daniel Amokachi brila
Talla

Hukumar ta ce, Amokachi ya samu nasarar ce bayan fafatawar da ya yi da wasu fitattun kociyoyi irin su Mike Emenalo da ya yi aiki da kungiyar PSG da Chelsea da Austin Eguavoen da ya jagorancin Super Eagles da Ladan Bosso da Sam Okpodu da kuma Mutiu Adepoju.

Amokachi wanda ya taba zama mataimakin Stephen Keshi wajen jagorancin Super Eagles zai gaji Bitrus Bewarang wanda ya kammala wa’adin aikinsa.

Tsohon tauraron dan wasan Najeriya Amokachi ya buga wa kungiyoyi da dama da suka hada da Ranchers ta Kaduna kafin ya tafi kasar Belgium, inda ya yi wa Clubb Brugge wasa kafin ya koma Everton da ke Ingila, inda ya lashe kofin kalubalen kasar.

Amokachi ya kuma yiwa Besiktas ta Turkiya da Colorado Rapids da ke Amurka wasa, kafin ya karkare a Nasarawa United.

Ya yi kuma aiki a matsayin mai horar da 'yan wasan Nasarawa United da Enyimba kafin ya koma Super Eagles domin taimakawa Stephen Keshi.

A makon jiya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Amokachi a matsayin Jakadan kasar kan harkokin kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.