Isa ga babban shafi
Wasanni

Nasararmu ta dogara kan dakile karsashin Neymar da Mbappe - Dortmund

Mai horas da kungiyar Borussia Dortmund Lucien Favre ya bukaci ‘yan wasansa da su zage damtse yayin fafatawarsu da PSG yau talata a matakin zagaye na 2 na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Yan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar da Kylian Mbappe.
Yan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar da Kylian Mbappe. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Favre ya ce makomar samun nasarar da suke fatan yi a wasan na yau, ya dogara ne da yadda ‘yan wasan Dortmund za su jajirce wajen kalubalantar zakakuran ‘yan wasan PSG da suka hada da Neymar da kuma Kylian Mbappe.

Wasan na yau dai shi ne farko da Neymar zai fafatawa kungiyarsa ta PSG, bayan rasa damar buga wasanni 4 a jere, sakamakon raunin da ya samu a hakrkari.

PSG dai na fatan samun nasarar kaiwa zagayen farko na siri daya kwale wato kwata final, na gasar ta zakarun turai karo na farko, bayan rasa damar yin hakan sau da dama a shekarun baya.

A bangaren Borussia Dortmund kuwa, kungiyar na fatan maimaita bajintar da suka yi a shekarar 2013, musamman la’akari da sabon dan wasan gaba da suka dauka Erling Braut Haaland mai shekaru 19, wanda cikin wasanni 6 kawai da ya bugawa kungiyar ya ci mata kwallaye 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.