Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta yi cefanen gaggawa

Barcelona ta kammala kulla kwantiragi mai cike da sarkakiya tare da dan wasan gaba na Denmark Martin Braithwaite daga Leganes a kan farashin Euro miliyan 15.

Martin Braithwaite da ya koma Barcelona daga Leganes
Martin Braithwaite da ya koma Barcelona daga Leganes Skysport.com
Talla

Hukumomin Gasar La Liga sun bai wa Barcelona izinin sayen dan wasan duk da cewa, an rufe kasuwar cefenen ‘yan wasan bayan Ousmane Dembele ya gamu da raunin da zai tilasta masa zaman watanni shida na jinya.

Dokokin La Liga sun amince wa kungiyoyin da ke buga gasar da su nemi izinin sayo sabon dan wasa muddin daya daga cikin ‘yan wasansu ya samu raunin da zai tilasta masa zaman jinyar sama da watanni 5.

Yanzu haka Braithwaite zai ci gaba da zama a Barcelona har zuwa karshen watan Yunin shekarar 2024.

Dan wasan ya zura kwallaye 8 a wasanni 27 da ya buga wa Leganes a wanann kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.