Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Cin kwallaye ya zama jiki ga Ronaldo - Messi

Dan wasan gaba na Barcelona, Lionel Messi ya ce bai yi mamakin yadda takwaransa Cristiano Ronaldo ke kan ganiyarsa wajen antaya kwallaye a raga ba a kungiyarsa ta Juventus, yana mai yabawa da yadda dan wasan gaban ke taba zare.

Shahararrun 'yan kwallo, Messi da Ronaldo.
Shahararrun 'yan kwallo, Messi da Ronaldo. Josep LAGO / AFP
Talla

Duk da cewa dan wasa, Ronaldo ya cika shekaru 35 da haihuwa a cikin kwanakin nan, kwallaye 11 ya ci wa kungiyar ta sa cikin wasanni 11 da ya buga a wannan wata a jere, kuma a wannan kaka yana da kwallaye 24 jimilla.

a waje daya kuma, wasanni 4 ne Messi ya buga a jere ba tare da ya saka kwallo a raga ba, amma ya taimaka an ci kwallaye 6 a wasanni 3 na baya bayan nan da ya buga wa kungiyarsa, Barcelona.

Ko da yake ‘yan wasan biyu gwanaye ne wajen cin kwallaye, Messi ya yi amannan cewa Ronaldo ya mayar da cin kwallo jiki a gareshi, saboda haka ya ce bai yi mamakin yadda dan kasar Portugal din ya ke zazzaga kwallaye a ragar abokan hamayya ba duk da wannan shekaru na sa.

Messi ya ce "Ronaldo yana da dabi’u da dama irin na dan wasan gaba, kuma yana da wuya ya yi arba da damar cin kwallo ya gaza ci."

Shi ma Messi ya ci kwallaye 14 a wasanni 19 da ya buga wa Barcelona a wannan kaka a gasar La ligar Spain, abin da ke nuni da cewa a matsayin sa na mai shekaru 32, dabara ba ta kare mai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.