Tokyo 2020: Coronavirus na neman kawo nakasu ga shirin China
Annobar coronavirus ta kawo cikas ga shirin fafatawa a gasar Olympics da ‘yan wasan guje – guje da tsalle – tsalle na kasar China ke yi, inda ta tilasta musu tsallaka wasu wasannin neman cancanta, sannan aka killace su wajen atisaye, wani lokacin ma sai sun sanya mayanin fuska.
Wallafawa ranar:
Masu shirya wasanni dai sun yi ittifakin cewa wannan annobar da ta bulla daga birnin Wuhan, ta kuma kashe mutane sama da 2100 ba za ta kawo nakasu ga wannan gasa da suke shirin tafiya ba.
Sai dai ana ganin mai yiwuwa ta yi mummunan tasiri ga tawagar kasar China, wadda a gasar Rio ta 2016 ta kunshi ‘yan wasa 416, kuma ke cikin ukun farko a duk gasanin da aka yi a wannan karnin.
Babu wanda ya kamu da wannan cuta dai a cikin tawagar ta kasar China, amma bullar annobar ta zo a wani lokaci mai mahimanci a shirin da suke na zuwa gasar da za a fara ranar 24 ga watan Yulin wannan shekarar.
Wani misali a nan dai shine, tawagar kwallon kafar mata ta China, ta koma yin atisaye a farfajiyar wani otel, wato Brisbane Otel, bayan an killace su gabannin wasan neman cancantar fafatawa a Olympics din.
China dai na fata takwarorinta za su bude kofofinsu ga ‘yan wasanta a yayin wasannin neman tikiti, inda tuni wasu kasashe, ciki har da Australia suka tsaurara bincike kan ‘yan China da ke shigowa kasashensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu