Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Akwai ayar tambaya a al'amarin na'urar VAR - Lampard

Korafe korafe sun dabaibaye gasar Firmiyar Ingila a Asabar, biyo bayan hukuncin da aka yanke ta wajen amfani da na’urar VAR.

Kocin Chelsea Frank Lampard
Kocin Chelsea Frank Lampard Reuters Blogs
Talla

Wasu sun ce wannan na’ura na iya illata kwallon kafa har abada, yayin da wasu ke cewa, hankali ba zai dau hukuncin VAR ba. Suna nuni ne da abin da ya faru a wasa tsakanin Chelsea da Tottenham.

Kocin Chelsea Frank Lampard ne ya fara fitowa karara ya yi korafi, inda ya ce akwai babbar ayar tambaya kan wannan fasahar, bayan rashin yanke wa dan wasan tsakiya na Tottenham, Giovani lo Celso hukuncin kora, sakamakon mugun rafka da ya yi a cikin fili a wasan na Lahadi.

Akwai ma wasu hukunce hukunce da na’urar VAR ta yi a wasan da Burnley ta doke Burnemouth da kuma nasarar da Man City ta yi a Leicester da ake ganin ba su yi daidai ba.

Tsohon mai tsaron ragar Manchester United Peter Schmeichel cewa ma ya yi, na’urar VAR za ta wargaza kwallon kafa.

A wannan kaka ne aka aka fara amfani da na’urar VAR a gasar Firimiya Ingila, amma har ta buwayi masoya wasan kwallon kafa, musamman magoya bayan kungiyoyi, wadanda suka ce akwai kura kurai a hukunce hukuncen ta, kuma lokacin da take dauka kafin yanke hukuncin yana rage armashin wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.