Isa ga babban shafi
Masarautunmu

Dalilan da suka sa Sarakuna basa sauka daga mulki a kasar Hausa kashi na 1

Wallafawa ranar:

Shirin Daga Masatun mu shiri ne da ke leka masarutun da suka shahara aduniya.Shirin na wannan makon, zai duba yadda wasu sarakuna a kasashen duniya, kan sauka daga gadon sarautar, don bar wa magadan su, su ci gaba da mulki kasar tasu.A kasar Belgium, Sarki Albert II ya sauka daga mukamin shi don radin kan shi, inda ya mika wa dan shi yarima Philippe, a cikin wannan shekarar.A dai cikin shekarar, Sarauniya Beatrix ta Hollanda, ta sauka daga mukamin ta inda ta mika wa dan ta Willem-Alexander madafun ikon masarautar.A kasar Qatar ma sarki Hamad bin Khalifa Al Thani, ya ajiye muklamin shi ya mika wa dan shi, Sheikh Tamim a cikin shekarar ta 2013.To wannan shirin zai duba dalilan da suka sa sarakunan kasar Hausa, basa yarda su bar gadon sarautar tun suna da rai.Prof Aliyu Muhammad Bunza, Malami a sashen koyar da Harsunan Najiriya, a jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sokoto, ya yi bayani kan wannan, don haka sai a biyo mu cikin shirin, da shine kashi na farko, Tare da Nasiruddeen Muhammad, don jin karin bayani.A yi saurare lafiya.

Mai martaba Sarkin Kano, Dr. Ado Bayero
Mai martaba Sarkin Kano, Dr. Ado Bayero
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.