rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ecuador

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Ecuado ta yanke hukunci kan tsohon Shugaban hukumar kwallon kafa

media
Yaki da karbar cin hanci da rashawa a Fifa FABRICE COFFRINI / AFP

Luis Chiriboga Tsohon Shugaban hukumar kwalon kaffa na Ecuado na fuskantar tuhuma kan zargin da ake masa na hada kai wajen karkata makudan kudade dama karbar na goro .
 


Kotun kasar ta yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon shekaru 10, ana kuma tuhumar sa da halita wasu kudade da ya karba ta hanyar da basu dace ba, haka zalika kotun kasar Ecuado ta yanke hukuncin daurin gidan maza na shekaru goma zuwa tsohon ma’ajin hukumar kwallon kafar kasar ta Ecuado Hugo Mora da mataimakin sa Pero Vera.
Luis Chiriboga ya shugabanci hukumar kwallon kafar kasar Ecuado daga shekara ta 1998 zuwa 2016.