rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Italiya Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa da Italiya za su tunkarar matsalar bakin haure

media
Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Italiya Paolo Gentiloni REUTERS/Max Rossi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Italiya Paolo Gentiloni, sun amince kasashen biyu za su aiki tare domin kara tunkarar matsalar kwararar baki da kuma sauran batutuwa da suka shafi tattalin arziki.

Wadannan na daga cikin abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna a ganawar da suka yi a birnin Roma na Italiya.


Shugaban Faransa ya bukaci ganin a rika bambantawa a tsakanin bakin-haure, ‘yan gudun hijira, masu neman mafaka da ma wadanda suka bar kasashensu saboda dalilai na tattalin arziki.

Kasashen Faransa da Italiya na fuskantar babban kalubale sakamakon yawaitar mutanen da ke neman samun mafaka a kasashen fiye da yadda suka taba ganin a can baya.

Wadanan kasashe na ganin cewa ya zama dole su dauki matakan da suka wajaba kan wannan matsala.

A shekarar da ta gabata, yawan wadanda suka bukaci izinin shiga Faransa kawai ya haura dubu dari daya, wannan adadi ne da ke tabbatar da cewa Faransa ba a rufe take ga baki ba.

Kasashen sun bukaci mutunta dokoki dangane da matakan da suka dau tareda kaucewa yi hannun riga da manufofinmu su.