rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sarkozy zai daukaka kara

media
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a a lokacin da yake kare kansa atashar TF1. Handout / TF1 / AFP

Nicolas Sarkozy da ya jagoranci kawancen kasashen da suka yaki mulkin Kaddafi wanda ya yin alkawarin zubar da jinni a Benghazi, ya musanta zargin da ake masa na karbar kudade daga hannun Libya a yakin zaben san a shekara ta 2007.

 


Sarkozy na magana ne a gidan talabijen na TF1 na kasar ta Faransa.

Nicolas Sarkozy a tashar TF1 na Faransa 23/03/2018 Saurare

Daya daga cikin na hannun damar tsohon Shugaban Libya Moftah Missouri ya gaskanta goyan bayan marigayi Kadhafi na  kudi milyan 20 na dala zuwa dan takara Nicolasa Sarkozy a shekara ta 2007.

Moftah Missouri daya daga cikin na hannun damar Kadhafi 23/03/2018 Saurare

Moftah ya bayyana cewa Sarkozy da Kadhafi sun yi haduwar farko ne a shekara ta 2005.

Lauyan tsohon Shugaban kasar Thierry Herzog ya sanar da aniyar su na daukaka kara.