Isa ga babban shafi
Masar

An soma kada kuri'a a zaben shugaban kasa a Masar

Daruruwan magoya bayan shugaban kasar Masar Abdel Fatah al Sisi suka yi tururuwa zuwa tashoshin zabe yau litinin, a zaben da ake ganin shugaban kasar zai lashe ba tare da matsala ba.Za’a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da wannan zabe.

Abdel Fattah al-Sissi dan takara  a zaben shugabancin kasar Masar
Abdel Fattah al-Sissi dan takara a zaben shugabancin kasar Masar EGYPT STATE TV/ via REUTERS
Talla

Motoci dauke da amsa kuwa sun yi ta zagaya birnin Alkahira suna kira ga al’ummar kasar da su fito don kada kuri’un su, yayin da suke sanya faya fayan soji da taken kasa.

Bayanai sun ce an dauki matakan tsaro mai tsauri a tashoshin kada kuri’un domin kaucewa duk wata barazanar da kan iya tasowa sakamakon ikrarin kungiyar dake tada kayar baya cewar zata hana gudanar da zaben.

Shugaba Al Sisis ya kada kuri’ar sa da misalin karfe 9 agogon kasar, a yankin gabashin Heliopolis, kamar yadda kafar talabijin din kasar ta sanar, yayin da abokin takarar sa Moussa ya kada kuri’ar sa a tsakiyar birnin Alkahira.

An dai zabi shugaba al Sisi ne a shekarar 2013, shekara guda bayan kifar da gwamnatin shugaba Mohammed Morsi, inda ya kwashe shekaru 5 a karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.