rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Qatar Falasdinawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron kungiyar kasashen Larabawa a Saudiya

media
Tambarin kungiyar kasashen Larabawa Probst/ullstein bild via Getty Images

Kwana daya da kaddamar da farmaki a Syria ,kasashen kungiyar larabawa na gudanar da zaman taro shekara da shekara a Saudiyya da ake somawa a yau lahadi.


Taron kungiyar kasashen larabawa a karkashin Shugabancin Saudiya,wannan karon zai mayar da hankali zuwa wasu manyan batutuwa da suka shafi diflomasiya tsakanin kasashen da Iran, yaki a kasar Yemen dama rikicin gabas ta tsakiya.

A daya geffen ,Shugabanin kasashen za su mayar da hankali tareda tsaida matsaya guda bayan farmakin da Amurka,Faransa da Birtaniya suka kaddamar zuwa Syria, duk da goyan baya da wasu kasashen larabawa suka nuna a kai.