rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha FIFA Spain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha ta doke Spain a gasar cin kofin Duniya

media
Fernando Hierro mai horar da kungiyar kwallon kafar Spain REUTERS/Stringer

Kasar Rasha tayi nasarar doke Spain a gasar cin kofin duniyar dake gudana yanzu haka, bayan sun tashi 1da 1 a mintina 90 ba tare da wata tayi galaba ba.


Bayan kammala karin mintina 30 ba tare da jefa kwallo ba, an tafi bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Rasha ta samu nasara da ci 4-3.

Wannan ya baiwa kasar damar zuwa zagaye na gaba, wanda zai bata damar karawa da kasar da ta samu nasara a karawar da akeyi yanzu haka tsakanin Croatia da Denmark.

Spain wadda ta lashe kofi a shekarar 2010 tabi sahun manyan kasashen da suka yi fice a harkar kwallon kafa irin su Jamus da Argentina da kuma Portugal wajen ficewa daga gasar.