Isa ga babban shafi
Turai

Faransa zata fafata da Croatia a gasar karshe na cin kofin Duniya na kwallon kafa

Yau ake karawar karshe a gasar cin kofin duniya ta bana dake gudana a Rasha inda kasar Faransa zata kece raini da Croatia.Kafin zuwa wannan mataki Faransa ta doke Belguim da ci 2-0, yayin da Croatia ta doke Ingila da ci 2-1.

Kungiyar kwallon kafar Faransa a Rasha
Kungiyar kwallon kafar Faransa a Rasha REUTERS/Henry Romero
Talla

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana cewa gasar cin kofin duniya ta bana da Rasha ke karbar bakunci a matsayin mafi kayatarwa a tarihi, yayin da magoya bayan kungiyoyin Faransa da Croatia ke ci gaba da sa kai zuwa filin wasan Moscow inda kungiyoyin biyu za su fafata domin ganin kasar da zata samu nasara.

Hukumomin Rasha da Faransa da Croatia duk sun sanar da daukar matakan tsaron da suka dace domin kaucewa duk wata barazana da kan iya dagula lamura.

A Faransa kusan yan Sanda 12,000 ne za suyi aikin samar da tsaro, yayin da aka sanya sojoji cikin damarar ko ta kwana domin ganin an magance duk wata barazanar dake iya tasowa.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yanzu haka ya isa Rasha domin ganewa idanun sa yadda wasan zai kasance, haka zalika fadar Shugaban kasar Faransa ta bayyana cewa Macron zai gana da yan wasan a gobe litinin a fadarsa dake birnin Paris.

Croatia da ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya na Rasha bayan ta doke Ingila da kwallaye 2-1.

Wannan shine karo na farko da Croatia take samun gurbi a yayin da Faransa ta lashe kofin a shekarar 1998.

Cikin zaratan ‘yan wasan da ake saran zasu taka rawa sosai a karawar yau sun hada da Paul Pogba da Antoine Griezeman da Kylian Mbappe daga Faransa, yayin da Luak Moderic zai jagorancin takwarorin sa irin su Mario Mandzuki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.